An maida Kwamishinan ‘Yan sandan Filato, kwana daya bayan cire shi

0

Rundunar ’Yan sandan Najeriya, ta bayyana maida Undie Adie a matsayin sa na kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato, kwana daya bayan maye gurbin sa da aka yi da Ciroma.

An yi wannan sanarwar maida Adie ne a yau Laraba, kamar yadda ya shaida wa Premium Times da kan sa.

A jiya ne dai aka maye gurbin sa da Bala Ciroma, bayan ya shafe watanni tara kacal ya na kwamishinan ‘yan sanda a Filato.

Shi ma kakakin ‘yan sanda na jihar, ya fitar da wata sanarwar da ke dauke da sake maida Adie da aka cire jiya.

Yayin da ake ta yada rudun cewa an tsige shi ne, ba cire aka yi da nufin maida shi wani wuri ba, sai kuma ga wata sanarwa cewa ya gaggauta komawa a kan mukamin sa a Filato, ya gaggauta karbar iko daga hannun Bala Ciroma.

Adie ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Sufeto Janar ne da kan sa ya yi tunanin sake maida shi a kan mukamin sa.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin kakain ‘yan sanda na kasa, Jimoh Mosheed, amma bai dauki waya ba. An tura masa sakon kar ta kwana, har zuwa lokacin rubuta wannan labari, Jimoh bai maida amsa ba.

Share.

game da Author