Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira da a dunga yi wa sabbin ma’aikatan da za a dauka a ma’aikatun gwamnati na kasar nan da daliban sakandare da Jami’o’i gwajin cutar tarin fuka kafin a ba su aiki.
Isaac ya ce yin haka zai taimaka wajen gane masu dauke da cutar da kuma magance yaduwar cutar a kasar nan.
” Bincike ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da cutar tarin fuka sannan daga ciki kashi 25 bisa 100 ne kadai aka iya gano wa.”
Ya ce mutane masu yawa ne ke rasa rayukan su a dalilin kamuwa da wannan cuta a kasar nan musamman a yankin Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
” Ina kira ga duk ma’aikata da ke jihohi da kananan hukumomin kasarnan da su dunga yi wa duk wani sabon ma’aikaci gwajin tarin Fuka, har da ma sabbin dalibai a makarantun mu domin kare sauran ma’aikata da ga kamuwa, wato a rage yaduwar cutar.
A karshe yace wannan dabaran za ta taimaka wa ma’aikatan kiwon lafiya wajen gano cutar a jikin mutane musamman wadanda ke dauke da ita basu sani ba.