Gwamnatin APC bata sake da PDP ba, duk kanwar ja ce -Falana

0

Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aikata laifin danne hakkin dan Adam kamar irin wanda APC suka rika zargin gwamnatin PDP na yi kafin ta hau mulki.

A cikin wata takardar bayani da ya aiko wa PREMIUM TIMES, Falana ya ce kafin APC ta hau mulki, ta rika kuka a kan yadda gwamnatin PDP ke tauye hakkin mambobin ta da na sauran jama’a ba gaira ba dalili.

“Idan kun tuna, ANPP da sauran jam’iyyun adawa da kuma ofishin mu na lauyoyi, mun kalubalanci yadda ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa a Kano, cikin 2003, suka tarwatsa taron ANPP, kuma muka kalubalanci magudin zaben 2003 a karkashin gwamnatin Obasanjo.

“An fesa wa Janar Muhammadu Buhari barkonon tsohuwa, aka tarwatsa su a bisa dalilin wai ba su nemi izni daga gwamnatin tarayya ba.”

ANPP dai na daga cikin jam’iyyun siyasar da suka rikide, suka zama APC a cikin 2014.

Falana ya ci gaba da bayar da labarin yadda suka rika jula-jula a kotu sun a nemar wa su Buhari ‘yancin su har na tsawon lokaci.

Ya kuma zayyana yadda dokar Najeriya a wurare da dama ta nuna cewa haram ne a tsare dan Najeriya sama da awa 48 ba tare da takardar umarnin tsare shi daga kotu ba.

Falana ya yi wannan magana ne dangane da kukan da kwamitin kare ‘yan jarida ya yi cewa SSS sun tsare wani dan jarida mai suna Jones Abiri, tun cikin 2016, ba tare da an kai shi kotu ba.

Wani dalilin kuma shi ne ganin yadda Babban Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce ai Jones Abiri ba cikakken dan jarida ba ne, domin ba shi da rajista da kowace gidan jarida a kasar nan.

Dangane da tsare Sanata Enyinnaya Abaribe kuwa, Falana ya ce kowa ya san cewa Abaribe ne ya tsaya belin Nnamdi Kanu, kuma kotu ta ce ya nemo shi duk inda ya ke.

Don haka babu ruwan SSS da tsare shi, magana ce ta kotu, ba ta su ba. Amma idan kuma sun ce ana zargin sa da laifin safarar makamai, kamar yadda ake cewa, to kotu ya kamata su kai shi, idan sun kama shi, ba wai su ci gaba da tsare shi ba.

Idan ba a manta ba, Falana ya sha ragargazar gwamnatin Buhari dangane da ci gaba da tsare Ibraheem El-zakzaky, duk kuwa da cewa kotu ta ce a sake shi, tun cikin 2016.

Share.

game da Author