Sunayen Ministocin Buhari da suka karkatar da guraben karo ilmin da CCECC ya ware wa ‘yan Najeriya ga makusantan su

0

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku wani labarin abin kunya, wanda wasu ministoci da manyan jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari suka handame gurabun da kamfanin gina titin jiragen kasa na kasar China, CCECC ya ware, domin matasan Najeriya su samu damar zuwa China yin karatu.

A yau kuma mun bankado muku sunayen ministocin da manyan jami’an, wadanda su ne suka rabe gurabun karo karatun ga ‘ya’yan su, ‘ya’yan dangin su, na abokan su da kuma kannen matan su.

1 – Karamin Ministan Harkokin Ilmi, Anthony Onwuka;

2 – Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung;

3 – Karamin Ministan Harkokin Lantarki, Suleiman Hassan;

4 – Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar;

5 – Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi;

6 – Ministan Gona, Audu Ogbe;

7 – Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ade Ipaye;

8 – Karamin Ministan Harkokin Jiragen Sama, Hadi Sirika;

9 – Karamar Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Aisha Abubakar;

10 – Ministan Harkokin Yankin Neja-Delta, Usani Usani;

11 – Ministan Fasahar Sadarwa, Adebayo Shittu;

12 – Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Udo Udoma.

Duk yawancin wadanda PREMIUM TIMES ta tuntube su domin su kare kan su, ko kuma ta tuntubi kakakin yada labaran su, sun kasa cewa komai.

Wasu kuma idan an kira ba su dauka, ko an yi musu sakon tes, ba su maido amsa. Duk sun yi shiru, wai malam ya ci shirwa.

Karanta labarin a shafin mu na Turanci: REVEALED: Full list of public officials who ‘hijacked’ CCECC railway scholarships

Share.

game da Author