Kisan Filato na ramuwar-gayya ne -Miyetti Allah

0

Shugaban Miyetti Allah ya bayyana cewa kisan mutane 86 da aka yi a Filato, zai iya zama na ramuwar-gayya ne, saboda wasu kashe-kashe da sace-sace da kalibun yankin suka rika yi wa Fulani, alhali gwamnati ba ta yi komai ba.

Shugaban Miyetti Allah na Arewa ta Tsakiya, Danladi Ciroma ne ya bayyana haka a safiyar yau Litinin.

“Wadannan hare-haren na ramuwar-gayya ne. Duk da cewa ba na goyon bayan kisan mutum, amma a gaskiya dole mu fadi gaskiya cewa mai yiwuwa wadanda suka kai harin fa ramuwa-gayya ce suka yi.”

“Fulani makiyaya sun rasa shanu sama da 300 a cikin makonni kadan da suka gabata. An kara kashe musu wasu 36, kuma duk matasan Birom ne suka yi kisan. Aka sake sace wasu 94 a kauyen Fan. Sai kuma aka sake sace wa Fulani wasu shanu 174.”

A wani rahoton kuma, Ciroma ya bayyana yadda dattawan kauyukan Riyom da shugabannin gargajiyar su ke boye wadanda ke kai wa Fulani hari, sun a hana jami’an tsaro kama su.

Ya bada labarin yadda wasu matasa da suka saci tulin shanun Fulani, suka gudu da su zuwa garin Mangu.

Ya ce jami’an sojoji sun bi su domin su kama su, amma suka hai wa sojojin hari, har suka harbe su.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati cewa matsawar idan ba a rika hukunta wadanda suka fara kai hari ba, to rikicin zai ki ci, ya ki cinyewa.

Tuni dai aka fara kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya kori shugabannin hukumomin tsaron kasar nan ya canja su da wasu.

Shugaban jam’iyyar ADP na jihar Filato, Nanyah Daman, ya yi wannan kira yau Litinin.

Mahukuntan Jami’ar Jos, sun gargadi daliban su da su yi kaffa-kaffa, kamar yadda wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abdullahi Abdullahi ya sa wa hannu.

PREMIUM TIMES ta lura cewa ba a bude yawancin kantuna da makarantu a Jos ba a yau Linitin. An kuma samu labarin yadda aka rika samun tashe-tashen hankula a wajen gari inda aka rika tare motoci ana kai wa masu ababen hawa hari.

Share.

game da Author