Da karfin jam’iyya zan yi amfani ba da tirsasawar Buhari ba -Oshiomhole

0

Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshimhole, ya bayyana cewa idan aka zabe shi ya zama shugaban jam’iyyar APC, zai tabbatar da cewa jam’iyya ce ke da karfin iko, ba wai zai tsaya sai yadda Shugaban Kasa ko wasu suka ce a yi ba.

APC za ta yi zaben shugabanni a ranar 23 Ga Yuni, a Abuja, inda za ta zabi shugabannin ta.

Adams Oshiomhole na a sahun gaba na masu takarar shugabancin jam’iyyar APC a zaman yanzu.

Ya ci gaba da cewa idan ya samu nasarar zama shugaba, zai tabbatar da cewa Shugaba Buhari da duk wani mai karfin fada a ji a cikin APC, to sai sun kwantar da kai sun bi tafarkin da jam’iyya ta tsara.

Oshimhole ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da wasu matasan jam’iyyar APC.

Ya ce fatan da ya ke yi shi ne ya samu nasara a ranar Asabar idan an zo zabe. Domin a ta bakin sa, duk wasu manyan rigingimu za su kau, saboda ba zai bari jam’iyya ta rika tafiya kara-zube ba

“Wato ni kallon da na ke yi wa APC shi ne, ba mu ma da wata babbar inuwa da za mu kira jam’iyya. Domin a baya ta-ci-barkatai ake gudanar da jam’iyyar. Saboda ba a tattauna duk wasu lamurra na jam’iyya a gaban wadanda ya kamata a ce sun tattauna batutuwan.”

Share.

game da Author