Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a matsayin gwarzon dimokradiyar Najeriya.
Atiku ya yi wannan kwarzantawa a wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Jonathan a garin su na Otuoke, jihar Bayelsa.
Atiku ya bayyana yadda Jonathan ya mika mulki salum-alum, ba tare da wani tashin-tashina ba.
Ya ce da Jonahan bai mika mulki a lokacin ba, to da yanzu labari ya sha bamban a kasar nan.
Ya ce ta-mazan da Joanthan ya yi a lokacin har ya yi gaggawar taya wanda ya zarce shi kuri’u murna, ya nuna cewa kyakkyawan halin kishin dimokradiyyar sa abin koyi ne, kuma da wuya a samu kamar sa.
Dama kuma tun da farko, a ziyarar da Atiku ya kai ga gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi kira ga APC cewa idan aka kayar da ita, to ta hakura kawai ta bayar da mulki, ba tare da wani ja-in-ja ba.
Jonathan ya yaba da yadda Atiku ya dauki Gbenga Daniel a matsayin daraktan kamfen din sa na neman takarar shugabancin kasa a zaben 2019.