Zan yi wa Buhari ‘Kifa Daya Kwala’ a zaben 2019 – Makarfi

0

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma dan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makrfi ya bayyana cewa tabbas idan har jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin Najeriya a 2019, ko haufi ba ya da shi cewa zai yi wa Buhari kifa daya kwala ne a zaben.

Makarfi ya fadi haka ne a ziyarar neman kuri’u daya kai jihar Filato.

A garin na Jos, Makarfi yace irin barakar da aka samu a kasar nan a tsawon mulkin jam’iyyar APC nuni ne cewa sun gaza kuma shine kadai zai iya murkushe su a zaben kasa da za ayi a 2019.

” Maganar tsaro dai shine a kan gaba. Ba za muyi kasa-kasa ba wajen ganin gwamnatin mu ta gano bakin zaren sannan ta kulle shi tamau inda ba za a sake jin umhum ba game da tsaro a kasar nan.

” Idan kuka duba, bayan rashin tsaro da tashin hankali da ake fama dasu, ga fitinan sace-sacen mutane da yaki ci yaki cinyewa. Wadannan duk abu ne da zamu magance su babu kakkautawa.

Shugaban jam’iyyar a jihar filato Damishi Sango ya tabbatar wa Makarfi cewa mutanen jihar za su mara masa baya don ganin ya sami nasara a zaben 2019.

” Mun ga irin kokarin da kayiwajen hada kan jam’iyyar mu, wannnan nuni cewa tabbas ka cancanci shugabanci kuma zaka iya domin kuwa Irin wannan jarumtan naka ne muke bukata mu fatattaki Buhari daga fadar gwamnati a 2019.”

Share.

game da Author