Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Raji Fashola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta gyara gadar Mokwa zuwa Jebba, wadda ta karye nan da kwanaki uku kacal.
Fashola ya bayyana wa manema labarai haka a Zari’a, jihar Kaduna, jim kadan bayan da ya kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau ziyara a fadar sa, ranar Lahadi.
Kafin ziyarar fadar Sarkin, sai da Fashola ya kaddamar da wata babbar na’urar kara karfin wutar lantarki, taransifoma, wadda za ta kara karfin wuta a cikin garin Zariya da kewaye.
Na’urar dai ta na da karfin 132KV.
Ya ce ma’aikatar sa ta tura kwararrun jami’ai daga ma’aikatar da ta kamata, domin kawo saukin cinkoson motoci a mahadar ta Gadar Mokwa zuwa Jebba, ya na mai cewa nan da awa 72 za a kammala gyara komai.
Hukumar Kiyaye Rayuka da Kare Hadurra, FRSC, ta bayyana cewa ruwa mai karfin gaske da aka yi ne ya karya gadar.
Gadar wadda ke da da nisan kilomita 18 da Mokwa jihar Neja, ta karye ne kuma kawo matsalar Jirga-zirgar motoci a dukkan bangarorin titin biyu, wanda ya hade Arewaci da Kudancin Najeriya.
Ita ce hanyar da matafiya dubbai ke bi daga Abuja zuwa garin Ilorin.