Kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa Ahmad Sajoh ya bayyana cewa wani yaro ya rasa ransa sannan wasu abokan sa biyu sun sami rauni sanadiyyar wani bam da ta tashi da su a garin.
Ya ce yaran sun tsinto bam din ne a wajen roreroren su, can suka tsinto wannan bam. Suna cikin dubawa kuwa ta tashi da wanda ya ke rike da bam din.
” Shidai wanda ya tsinci bam din ya sheka lahira nan take sauran kuma sun sami rauni.”
Sajoh ya ce tuni sun gano iyayen yaran, sannan wadanda suka sami rauni a harin suna asibiti ana duba su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar ya gargadi iyaye da su sa ido wajen sanin inda ‘ya’yan su ke kurde-kurden su a gari da inda suke zuwa.
” A rabu da yara na gararamba a gari babu kula na da hadari sosai.
Discussion about this post