Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Raji Fashola, ya kaddamar da wata babbar na’urar kara karfin wutar lantarki, taransifoma, wadda za ta kara karfin wuta a cikin garin Zariya da kewaye.
Na’urar dai ta na da karfin 132KV.
Fashola ya bayyana wa manema labarai haka a Zaria, jihar Kaduna, jim kadan bayan da ya kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau ziyara a fadar sa, ranar Lahadi.
Bayan haka Fashola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta gyara gadar Mokwa zuwa Jebba, wadda ta karye nan da kwanaki uku kacal.
Ya ce ma’aikatar sa ta tura kwararrun jami’ai daga ma’aikatar da ta kamata, domin kawo saukin cinkoson motoci a mahadar ta Gadar Mokwa zuwa Jebba, ya na mai cewa nan da awa 72 za a kammala gyara komai.
Ita ce hanyar da matafiya dubbai ke bi daga Abuja zuwa garin Ilorin.