Fursinoni 200 sun arce daga kurkukun Minna

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da guduwar wasu fursinoni 200 daga kurkukun dake Minna ranar Lahadi.

Kwamishina Dibal Yakadi ya fadi haka ranar Litini a Minna.

Ya bayyana cewa hakan ya auku ne a dalilin far wa gidan yarin da wasu barayi suka yi da karfe takwas na daren Lahadi.

Yakadi yace ‘yan sandan sun kama wasu 19 daga cikin 200 da suka gudu sannan ma’aikacin gidan yari daya ya rasa ransa.

” Za mu hada hannu da sauran jami’an tsaro dake jihar domin ganin mun kamo sauran. Sannan ya roki mutanen gari da su taimakawa wa ‘yan sanda don ganin an kamo su.

Share.

game da Author