Mahara sun kashe mutane uku a harin Filato

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane uku a kauyen Kura Fall dake karamar hukumar Barkin Ladi.

Kakakin rundunar Terna Tyopev ya sanar wa PREMIUM TIMES ta sakon waya ranar Asabar.

” Mun sami labarin wasu mahara sun kai wa kauyen Kura Falls hari ranar Juma’a da karfe 9:30 na dare zuwa safiyar Asabar. Mutane uku sun rasa rayukan su a wannan hari.

Wadanda suka rasa rayukan su sun hada da wani mai suna Dawala Bullet mai shekaru 30, Fidelis Richard mai shekaru 31 da wani tsoho Iliya Doro mai shekaru 60.”

Tyopev yace tuni jami’an ‘yan sanda sun fantsama domin nemo wadannan mahara.

Bayyanai sun nuna cewa duk da ‘yan sanda da sojoji da a girke a yankin Kaduna da Filato basa rabuwa da hare-haren daga wadannan muggan mutane.

Share.

game da Author