An bankado akalla wasu kwangiloli har 34 na sama da naira biliyan 11.5 da Ministar Harkokin Kudade ta biya, alhali akwai umarnin da Shugaban Kasa ya bayar cewa kada a yi kwangilolin. PREMIUM TIMES da UDEME ne suka bankado dabakalar.
Dukkan wadannan kwangiloli an ce an yi su ne a ma’aikatun gwamnati daban-daban, kuma su na cikin kwngilolin da Fadar Shugaban Kasa ta ce wa Majalisar Tarayya a cire su kada a yi aikin a cikin kasafin 2017.
Akwai kwafen takardu a hannun PREMIUM TIMES da suka tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Mataimakin sa, Yemi Osinbajo duk sun sanar da cewa a cire ayyukan daga cikin Kasafin Kudin 2017.
Dukkan ayyukan 34, irin ayyukan cuwa-cuwa din nan ne da Mambobin Majalisar Tarayya suka cusa a cikin kasafin 2017, a gefe daya kuma suka cire wasu muhimman ayyukan raya kasa da ma’aikatu suka rattaba niyyar yi a cikin kasafin.
Majalisar Zartaswa dai ta ce ba za ta iya biyan kudaden ayyukan da ‘yan majalisar suka cusa ba, tunda sun cire ayyuka mafi muhimmanci da ya kamata a yi wa jama’a.
YADDA SUKA CUSA AYYUKAN ASARKALA A KASAFIN 2017
Rikici ya taso bayan maida kasafin 2017, yayin da wasu ministoci suka bankado cewa ‘yan majalisa sun cire wasu muhimman ayyukan da suka rattaba za a yi wa al’umma, sannan suka cusa ayyuka har 34 wadanda majalisa din ke so a yi, kuma ta hannun su za a biya kudaden.
Wannan kuwa wata karkatacciyar hanya ce da suka shigo da ita ta yadda za su rika azurta kan su a saukake, ba da gumin goshin su ba.
Dama sai da Ministam Ayyuka Tunde Fashola ya ce yadda ‘yan majalisar suka yi rashin adalci ne domin sun yi asarkalar ayyukan na su bayan ministocin sun je sun kare kasafin na ma’aikataun su.
Idan za a iya tunawa a wancan lokacin an yi ta nuna juna da yatsa, tsakanin majalisa da Minista Fashola, duk a kan batun kasafin kudi, su na sukar juna da shigo da salon ‘yar-burum-burum a cikin kasafi.
Shi ma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da Mistan Lafiya, Isaac Adebowole sun yi irin korafin da Fashola ya yi.
Ganin Yadda Majalisa da ministocin ke ta sa toka sa-katsi ne, ya sa Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kira taron tantance barcin makaho tsakanin majalisa da ministoci.
A lokacin Buhari ya na Landan. A ranar 18 Ga Yuli, 2017, Osinbajo ya rubuta wa Majalisa cewa a cire duk wadannan ayyuka 34 da majalisa ta sarkala a cikin kasafin 2017.
Osinbajo ya maida cewa ma’aikatu 15 su kawo ayyuka na adadin naira biliyan 136, domin a cike gurbin wadanda aka cire da majalisar ta cusa ba boye.
Osinbajo ya yi kira ga majalisa da ta gaggauta amince da ayyukan tunda dukkan sun na raya kasa ne.
PREMIUM TIMES ta gano cewa daga baya Osinbajo ya yi bibiyar majalisa har tsawon watanni domin su amince, amma suka yi watsi da shi. A nan ne ya gano cewa ramuwar-gayya suke so su yi kenan.
YADDA MA’AIKATAR KUDI TA KETA UMARNIN FADAR SHUGABAN KASA
Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta na cikin wadanda aka yi zaman tattaunawa da su, da shugabannin majalisa da kuma Mataimakin Shugaban Kasa.
Kuma ta fi kowa sanin cewa akwai umarni daga Fadar Shugaban Kasa cewa Majalisa ta gaggauta cire wadannan ayyuka 34 da suka yi wa asarkala a cikin kasafin 2017.
Duk da haka ta rufe ido, ta kauda kai daga umarnin Fadar Shugaban Kasa, ta rika sakar wa ‘yan kwangilar da majalisar dattawa ta ce su ne ke yin aikin makudan kudaden ayyukan da Gawamnatin Najeriya ta haramta a yi.
Kudaden da ta biya ba bisa ka’ida ba, sai a bisa izgili da galatsi, sun haura naira biliyan 11 ga ma’aikatu daban-daban, ciki har da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Dukkan wadandan kudade da ayyuka, sai aka jefa su a karkashin fannin ayyukan Inganta Kanana da Matsakaitan Masana’antu, wato SMEDAN.
Hukumar SMEDAN a tsakanin 2013 zuwa 2017 ta kasance wani wawakeken ramin da ‘yan majalisa ke amfani da shi suna cikewa da makudan kudade, daba baya kuma su bi dare su kwashe kayan su.
Duk wani dan Majalisar da ke so ya yi wa jama’ar yankin sa aiki, sai ya karkata a aikin a karkashin Hukumar SMEDAN, saboda ita ce hukumar da ta zame musu karkatacciyar bishiyar kuka, mai saukin hawa.
Duk wani aikin da ba a iya tantance shi kuru-kuru a ido, kamar yi wa mata da matasa horo, sai a ce duk an yi shi ko da ba a yi ba.
Ko kuma a yi aikin amma a kara yawan adadin wadanda aka bai wa horon.
An ce wai an yi wasu ayyuka har 13 daban-daban amma duk aka ce bai wa mata da matasa horo ne ayyukan.
A Ma’aikatar Ayyuka, Makamashi da Gidaje ma haka ‘yan majalisa suka yi haramben aiki na sama da naira bilyan 2.
Daga ka yi aikin kafa hasken sola, sai gina rijiyoyin burtsatse, sai kuma gina kwalbatoci kawai.
An kuma yi irin haka a Ma’aikatar Sadarwa, inda ‘yan majalisa suka cusa ayyuka na naira milyan 684, uku daga cikin su a jihar Oyo na naira milyan 664, sai kuma na milyan 20 a jihar Kebbi.
Can a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ma an yi wa naira milyan 50 fasaha a Ma’aikatar Gona kuwa, naira bilyan daya aka yi wa noman rana daya.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Ministar Hrkokin Kudade, amma wani hadimin ta mai suna Oluyinka Akintunde ya ce ba ta kasar. Kuma irin wannan magana ministar ce za a iya tunkara, ba wani hadimin ta ba.
Shi ma Kakakin Yala Labarai na Majalisar Tarayya, Abdulrazak Namdas, da takwaran san a Majalisar Dattawa, Sabi Abdullahi,
Duk ba su yi magana ba.
Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ya ce bai ma san cewa ma’aikatar kudade ta ki bin dokar Fadar Shugaban Kasa ba, har ta biya kudaden kwangilar da aka hana gudanarwa.
Amma ya ce za su bincika.
Ba wannan ne karon farko ko na biyu da Ministar Kudade yay i irin wannan sakala-sakala ba. Wattanin baya PREMIUM TIMES ta bankada wata harkallar sakin bilyoyin kudade ga ‘yan kwangilar Majalisa wadanda yawancin su kamfanonin bogi ne.
Kada a manta, an zarge ta da korar Shugaban Hukumar Kula da Hannayen Jarin Kamfanoni, Munir, saboda ta fahimci ya na kokarin ya fallasa wata harkalla da ta dabaibaye kamfanin mai na Oando, wanda Adeosun ke ganin cewa idan hakan ta faru, zai iya kwance mata zani a kasuwa.
Discussion about this post