Mahara sun kashe mutane 15 a Zamfara

0

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Muhammed Shehu ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane 15 a kauyen Zakuna dake jihar Zamfara.

Shehu ya fadi haka ne ranar Asabar a Gusau da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Shehu yace maharan sun far wa kauyen Zakuna ranar Juma’a da safe inda suka sace shanun mazaunan kauyen.

” Yayin da hakan ke faruwa sai ‘yan bangan kauyen wanda aka fi sani da ‘Yan sakai’ suka fatattaki maharan. Abin bai yi musu dadi ba aiko ‘yan ta’addan su koma suka kara shiri, wannan karon da suka dawo sai da suka kashe mutane 15 wanda duk ‘yan sa kai.

Ya kuma yi kira ga mazaunan kauyen da su taimaka wa jami’an tsaron da bayanan da suka san zai taimaka wurin kama wadannan mutane.

Bayyanai sun nuna cewa bayan mutane 15 da ‘yan ta’addan suka kashe a kauyen Zakuna, a makon jiya, irin wadannan ‘yan ta’adda sun kashe mutane 26 a wani kauyen jihar.

Share.

game da Author