ZABEN EKITI: APC su yi shirin kwashe kashin su a hannu – Inji Atiku

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa tabbas babu abin da zai hana APC bata kwashi kashin ta a hannu ba a zaben gwamnan jihar Ekiti da za ayi a watan gobe.

Atiku ya ce dole kuma su yi shirin amincewa da sakamakon zaben idan akayi domin kuwa PDP ce zata samu nasara a zaben.

Atiku ya yi wannan tsokaci ne a ziyar da ya kai jihar Ekiti tare da wasu gaggan ‘yan jam’iyyar a ci gaba da kamfen da ‘yan takarar gwamnan jihar da suke yi a fadin jihar.

” Wannan zabe dai dole duk wanda ya ci abashi kada ayi tunanin yibwa mutane murdiya domin ko hakan ba zai yi tasiri ba musamman ganin cewa dole ayi koyi da yadda PDP ta yi wa dimokradiyya ta saki mulki a 2015.

A jawabin sa gwamnan jihar Ayo Fayose cewa yayi babu wanda ya isa ya murde zabe a jihar.

” Muna tare da jama’a kuma mu za suyi, zamu zuba ido mu ga ta inda za su murde mana zabe. Ida n ma suna ganin za su iya toh sai dai a wata jihar amma ba a nan ba.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gbenga Daniel, Atiku Abubakar, David Mark, Ibrahim Shekarau, Ike Ekweremadu da sauran su.

Za ayi zaben Ekiti ranar14 ga watan Yuli mai zuwa.

Share.

game da Author