Maida 12 Ga Yuni ranar dimokradiyya, babban laifi ne – Lauya

0

Fitaccen lauyan nan da ya yi suna wajen kare hakkin dan Adam, Olisa Agbakoba, ya bayyana cewa maida ranar 12 Ga Yuni da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta zama ranar dimokradiyya a Najeriya, babban laifi ne.

Sai dai kuma ya ce duk da haka, ba zai garzaya kotu domin ya tafka shari’a wannan danyen hukunci da Buhari ya yi ba, saboda ganin yadda jama’a suka karbi batun da hannu biyu.

Shugaba Buhari ne ya maida ranar dimokradiyya daga 29 Ga Mayu, zuwa 12 Ga Yuni, ranar da aka yi zaben da aka yi ikirarin MKO Abiola ne ya lashe, amma ba a bayyana ba, wato 12 Ga yuni, 1993.

Agbakoba, wanda ya na daya daga cikin manyan bakin da gwamnatin Buhari ta gayyata a wurin karrama iyalin Abiola a fadar shugaban kasa,

Ya ce sauya ranar dimokradiyya din da aka yi tabbas kuskure ne kuma babba, amma tunda jama’a da dama sun nuna karbuwar canjin ranar, don haka ba zai garzaya kotu ba.

Agbakoba, wanda ya taba rike shugabancin Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, ya bayyana ra’ayin sa ne a lokacin da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a jiya Litinin.

“Ban ga amfanin sauya ranar ba, domin babu wani amfani.”

Matsayar da Agbakoba ya dauka, ta yi daidai da matsayar da Tsohon Cif Jojin Najeriya, Alfa Belgore ya dauka, inda shi ma ya haramta sauya ranar dimokradiyya zuwa 12 Ga Yuni da Buhari ya yi.

Share.

game da Author