TAKARAR GWAMNA: Sharri ne aka yi wa Magu -EFCC

0

Hukumar EFCC ta yi tir da abin da ta kira labaran kad-da-kanzon-kurege da ake yadawa cewa Shugaban ta Ibrahim Magu na da muradin tsayawa takarar gwamna.

EFCC ta ce Magu na tunanin maka kafar yada labaran da ta ruwaito cewa ya na neman kujerar gwamna.

Jaridar 247ureports.com ce ta buga labarin cewa Buhari ya yi ganawar sirri da Ali Modu Sheriff da nufin a bude wa Magu kofar tsayawa takarar gwamnan jihar Barno.

Rahoton da kafar yada labaran ta buga dai ya nuna Magu zai nemi takarar gwamna ne domin ya yi zilliya daga tsoron damkewa idan ya gama shugabancin EFCC, saboda ya jefa kansa cikin barankyankyamar da za ta kai shi kurkuku.

A kan haka ne EFCC ta ce labarin karya ce, sharri ne kuma kullalliyar bata suna da darajar da Magu ya dade ya na gina wa kan sa ce.

Ta ce Magu ba dan siyasa ba ne, kuma babu ruwan sa da neman zama gwamna.

Tuni dai Magu ya ce ya lura da yadda kafar yada labaran ke ta bata masa suna. Don haka ya yanke shawarar neman hakkin sa a kotu kawai.

Ya ce duk sauran jaridun da suka dauki labarin suka buga, har da su zai maka kotu.

Share.

game da Author