Kungiyar Red Cross na taimakawa marasa lafiya a jihar Sokoto

0

Kungiyar jinkai na ‘Red Cross Society of Nigeria’ ta tallafa wa likitocin asibitocin jihar Sokoto da wuraren kula da marasa lafiya a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta rawaito cewa tun daga ranar litini wani jami’in kungiyar Hussaini Yahaya ke taimaka wa marasa lafiya wurin ganin likita a asibitin ‘Specialist Hospital’ dake jihar Sokoto.

Yahaya yace a rana ya kan tallafa wa marasa lafiya 150 zuwa 170 don ganin likita a asibitin sannan tun da suka fara aikin daga ranar Litini mutum daya ne kawai ya rasu.”

Kungiyar na tallafawa likitocin dake asibitin Maryam Abacha da asibitin Usmanu Danfodio dake jihar.

A karshe Jami’in harka da jama’a na ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Sokoto Ibrahim Iya ya fadi cewa tabbas ma’aiktan lafiya a asibitocin jihar sun bi sahun sauran na sauran jihohi yajin aikin da kungiyar JOHESU take yi.

Share.

game da Author