Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Adamawa Bwalki Dilli ya sanar cewa mutane 12 sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar kwalara a jihar.
Ya sanar da haka ne ranar Talata da yake ganawa da manema labarai a Yola.
Dilli ya bayyana cewa cutar ta bullo a kananan hukumomi biyu dake jihar wanda ya hada da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu.
” Mun gaggauta zuwa wadannan kananan hukumomi ne bayan mun sami rahotan cewa ana zaton mutane 134 sun kamu da cutar sannan daga ciki 12 sun rasa rayukansu.”
” Bisa ga gwajin da muka yi a kananan hukumomin mun gano cewa mutane 11 ne suka kamu da cutar.
A karshe Dilli ya ce ma’aikatar kiwon lafiya da kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) sun bude wuri na musamman domin kula da wadanda suka kamu da cutar a Mubi sannan ya yi kira ga mutane da su tabbata suna tsaftace muhallin su da abincin da suke ci domin guje wa kamuwa da cutar.
Ya kuma bada wasu lambobin waya da za a iya kiran su da shi kamar haka 08031230359 da 07080601139 ko da wani ko wasu sun kamu da cutar a jihar.