Jami’in hukumar bada agajin gaggawa na jihar Gombe (SEMA) Danlami Rukuije ya bayyana cewa a sanadiyyar ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a daren Litini tayi ajalin mutane uku sannan gidajen 20 sun fadi.
Rukuije ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai ranar Talata a garin Gombe.
” Limamin masallacin Al-Burhan da Ladanin wannan masallaci na daga cikin mutane uku da aka rasa sannan mutane takwas sun sami rauni.
” Wuraren da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Jekadafari, Nasarawo da Tudun-Wada.”
Discussion about this post