Ministan Kwadago da Ma’aikata, Chris Ngige, ya bayyana cewa batun karin albashin da aka yi zaton za a iya aiwatarwa a cikin Satumba, ba zai iya yiwuwa ba.
Ngige ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata, a gidan sa na Abuja, ya na mai cewa watan Satumba dai kawai shi ne watan da ake sa ran cewa za a kammala cimma yarjejeniyar da za a iya kai ga wata matsaya guda kawai.
“Ana dai sa ran cewa Kwamitin Tattauna Mafi Karancin Albashi zai kammala ayyukan sa nan da watan Satumba, sannan ya damka wa gwamnatin tarayya domin a duba a yi abin da ke yiwuwa, daga nan kuma sai a mika kudirin da aka zartas ga Majalisar Tarayya.”
Ministan ya ce kwamitin na aikin jin ra’ayoyin jama’a kama daga jihohi da kamfanoni masu zaman kan su, domin cimma matsaya daya.
Sai ya kara da cewa yayin da kwamitin ke rangadin jin ra’ayin jama’a, jihohi da dama sun gabatar da matsaya mabambanta da juna.
Ya ce wasu jihohin na so mafi kankantar albashi ya tsaya a naira 22,000, wasu kuma har zuwa naira 58,000.
A ta bakin Ngige, ya ce su kuma gwamnoni sun tsaya kai-da-fata cewa muddun ana so a yi karin albashi, to sai an kara wa jihohi da kananan hukumomi kason kudaden da gwamnatin tarayya ke ba su a duk wata.
“Kai akwai ma wasu jihohin da ke ganin cewa kamata ya yi a bar mafi karancin albashin a yadda ya ke a naira 18,000, idan aka yi la’akari da yadda wasu jihohi da yawa ba su ma iya biyan albashin.” Inji Ngige.