Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa wasu barayin shanu sun kashe mutane kuma sun sace shanu a kauyen Kurega dake karamar hukumar Chikun a jihar.
Kakakin rundunar Mukhtar Aliyu, da ya sanar da haka ranar Talata ya bayyana cewa sun sami labarin cewa a ranar barayin sun far wa wannan kauyen ne da karfe biyu na rana inda suka kashe mutane uku nan take sannan hudu kuma suka tsira da rauni a jikin su.
Bayan haka wani mai unguwar kauyen mai suna Sardauna ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa haka kawai barayin shanun suka far musu inda suka sace shanun fulanin da ke zama da su sannan suka kashe mutane takwas.
Wani cikin ‘yan bangan dake kauyen ya bayyana cewa fun fatattaki barayin a lokacin da suka far wa kauyen.
” Sai dai sun kashe wasu ‘yan banga uku a cikin dajin da suka fita farauta sannan da yawa daga cikin su sun gudu da raunin harsashi a jikin su.”