BUHARI KO OBASANJO: Wa karfin wutar lantarki zai fizga?

0

Furucin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, inda ya zargi Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo da danne zunzurutun kudi har dala biliyan 16 da a harkar inganta hasken wutar lantarki, bai yi wa Obasanjon dadi ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai wasu muhamman tambayayin yadda zunzurutun kudade har dala bilyan 16 suka salwanta a hannun Obasanjo, da nufin aikin samar da hasken lantarki a Najeriya.

Buhari ya fadi haka ne a jiya Talata, a Fadar Shugaban Kasa, yayin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Magoya Bayan Buhari, karkashin jagoranci Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Hameed Ali.

Duk da dai gugar zana Buhari ya yi, bai ambaci suna ba, amma furucin cewa: “Ina maganar harsken lantarki a lokacin a shugaban kasa na lokacin ya yi ikirarin kashe dala bilyan 16 kan hasken wutar?”

A lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne daga 1999 zuwa 2006, aka kashe dala bilyan 16 a batun hasken lantarki.

Cikin martanin da Obasanjo ya maida wa Buhari a jiya da dare, ya ce idan Buhari dan dagaji ne, bai iya karatu ba, to ya ba ‘yan barandar sa littafin da shi Obasanjo ya rubuta, mai suna “My Watch,” da ya ce duk bayanin yadda aka yi aikin hasken wutar lantarki ya na ciki.

Obasanjo ya ce a je a bude “My Watch” a shafi na 41, 42, 43 da kuma 44, duk za a samu bayanan.

Sannan kuma ya ce ai an kafa kwamiti tun kafin ya sauka sannan kuma EFCC ta bincike shi tun ya na kan mulki, amma ba a same shi da laifin komai ba.

ASALIN RASHIN JITUWAR BUHARI DA OBASANJO

A ranar 23 Ga Janairu, 2018, an wayi gari da rudanin wasikar da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, wadda a cikin ta ya nuna dalilan sa na cewa Buhari ya kasa yin ko da rabin abin da aka yi tsammani idan ya hau shugabancin kasar nan zai yi.

Har ila yau, babban abin da wasikar dai ta kunsa a takaice shi ne kada Buhari ya sake tsayawa takara domin idan ya yi hakan, kamar Najiriya za ta sake wasu shekaru hudu ta na tafiya da-baya-baya.

Tun daga ranar da ya rubuta wa Buhari wasika, har yau Obasanjo bai sake sassauta wa Buhari ba. Har ta kai shi ga kafa wata kungiya mai suna Gamayyar Kungiyoyin Ceton Najeriya, wadda ake wa kallon cewa za ta rikide ta koma jam’iyyar siyasa. Ko da yake ana ganin sabuwar jam’iyyar SDP ita ce ta za kasance makamin su Obasanjo a jam’iyyance.

Kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla. An ce ita ce abu na karshe da ya tunzura Obasanjo har ya rubuta wannan wasika a ranar 23 Ga Janairu, 2018.

Rahotanni sun ce Obasanjo ya so a ba wasu kamfanoni da ya nemi ya kawo wannan kwangila ta tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla, amma aka nuna masa cewa a’a. Obasanjo ya rika kallon kan sa a matsayin daya daga cikin gaggan da suka kafa APC kan mulki, don haka duk abin da ya nema, to ya kamata a yi masa kawai.

Ya so Buhari ya yi amfani da karfin ikon sa na Shugaban Kasa, ya hana Ministan Makamashi bai wa wasu kamfanoni kwangilar domin a bai wa kamfanonin da Obasanjo ke so ya kawo, amma Buhari bai yi masa hakan ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa Obasanjo ya damu da harkar kwangilar Mambilla sosai, domin a ranar 19 Ga Augusta, 2017 ya kai ziyara har wurin da za a gina tashar samar da hasken lantarkin a Mambilla. Daga wurin ya koma garin Jalingo inda har ya bayyana wa manema labarai cewa ya kai ziyara wurin ne domin kashin-kansa. “Ku ma na ga wannan wuri cewa zai yi kyau sosai da samar da harken lantarki a wurin. Don haka ya kamata a gaggauta fara aikin nan, domin idan ma ba a yi aikin nan a yanzu ba, to nan gaba tilas sai an samar da wannan tasha ta samar da hasken lantarki domin amfanin ta ga kasar nan.” Inji Obasanjo.

ZARGIN SALWANTAR DA DALA BILIYAN 16

Ganin yadda abu ya kai tsamari a jiya tsakanin Buhari da Obasanjo, masoya Buhari na jinjina masa tare da saurin yanke hukuncin cewa Obasanjo ya salwantar da kudin.

Su kuma magoya bayan Obasanjo da ‘yan adawa na cewa kullumm Buhari sai bada uziri ya ke yi, tare sauri dora laifi ga gwamnatin baya. Hasken lantarkin da Buhari ke cewa an samu a yanzu, sun ce da dan Karen tsada kamfanoni, jama’a da talakawa ke shan wutar, sabanin alkawarin da Buhari ya yi cewa zai samar da hasken lantarki a saukake.

Da yawa kuma ganin cewa akwai yankunan karkara da aka sa wa hasken lantarki tun lokaci mulkin Umaru ‘Yar’adua, amma ta lalace, har yau mulkin Buhari bai farfado musu da wutar ba.

Fitattacen mai yin sharhin nan a jaridu da kafafen soshiyal midiya, Dakta Nura Alkali, ya warware zare da abawar wannan tankiya da ake yi tsakanin Buhari da Obasanjo.

A cikin na sa sharhin, Alkali, wanda mashahurin likitan kwakwalwa ne da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, ya yi bayani kamar haka:

Shin yaya gaskiyar lamarin zargin da Buhari ya yi cewa: “Gwamnatin Obasanjo da kashe kudi har dala bilyan 16 wajen kokarin inganta hasken lantarki, amma babu wani abin da za a iya nunawa an yi da kudin?”

BINCIKE:

1. Lokacin da Obasanjo ya hau mulki cikin 1999, Najeriya na da tsahoshin samar da hasken lantarki guda 7, kuma duk su na aiki. A lokacin su na samar da karfin makamashi miga wats 1,500. Tashoshin su ne na Kainji, Jebba, Shiroro, Egbin, Afam da na Sapele.

2. Ya samu tashoshin samar da makamashin kwal na Orji da na Ijora duk ba su aiki, saboda rashin kwal din sannan kuma kayan aiki a masana’antar sun zama tsoffin yayi.

3. Tsakanin 1999-2007, gwamnatin tarayya a karkashin Obasanjo ta gina tashoshin samar da makamashi, ko karfin hasken lantarki za su kai shida. Kuma a yanzu duk su ne ke samar a wuta ga babbar tashar tattara karfin wuta ta kasar nan. Wadannan tashoshi da Obasanjo ya gina kuma har yanzu su ke aiki, sun hada da:

Tashar Afam II, Tashar Lantarki ta Papalanto, Geregu, Omotosho, kuma duk ya zuwa watan Mayu, 2007 da Obasanjo ya sauka duk an kammala su. Gaba dayan su daga mai samar da karfin miga wats sama da 200, sai mai sama da 300, har zuwa mai samar da sama da 500.

4. A lokacin ba a kammala tashar karfin lantarki ta Alaoji a jihar Delta ba. Ta shida din kuma, wato ta Ikot-Abasi, a Jihar Akwa-Ibom, hadin guiwa ce tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya.

5. Tsakanin 1999 din nan kuma zuwa 2007, an kirkiro batun karin wasu tashoshin harken lantarki, ko makamashi a Sapele, jihar Delta. Sai kuma Egbema a jihar Imo. Sai Ehobor a jihar Edo, Gbaram a jihar Bayelsa, Calabar a jihar Cross-River da kuma ta garin Omoku cikin jihar Rivers.

6. Cikin shekarun 1999 zuwa 2007, gwamnatin Obasanjo ta gyara tashoshin hasken lantarki na Kainji da Shiroro, wadanda kafin lokacin kusan sun nemi su durkushe, saboda an yi watsi da su a baya.

7. Cikin shekarun 1999 zuwa 2007 an kirkiro wasu ayyukan hasken lantarki, wadanda sai bayan 2007, bayan Obasanjo ya sauka ne aka fara su, bayan da majalisa ta kafa dokar da ta bayyana su a matsayin kadarar gwamnati da za a saida. An sai da hannun jarin, inda Hukumar Hasken Lantarki ta tashi daga NEPA zuwa PHCN.

A TAKAICE:

A yau Najeriya na samun akalla miga wats 2,520 daga cikin tashoshin hasken wutar da gwamnatin Obasanjo ta kafa tsakanin 1999 zuwa 2007. Wadannan ba su cikin lissafin wasu ayyukan samar da wuta na hadin guiwa tsakanin kamfanoni masu zaman kan su da gwamnati, wadanda aka fara bayan 2007.

DAGA KARSHE:

Gwamnatin Obasanjo na da abin da za ta nuna da zai tabbatar da cewa ta yi aikin hasken lantarki. Ya rage ga masu bincike, injiniyoyi da kwararru su dauki kwakuleta, domin su gano cewa aikin ya ci dala bilyan 16 da ake cewa ko kuwa?

TAMBAYA: Shin a ina Buhari ya samu bayanin cewa babu abin da aka tsinana da har za a iya nunawa?

Share.

game da Author