Asibitin gwamnati dake Abuja ta maye gurbin masu yajin aiki da Sabbin ma’aikata

0

Asibitin gwamnatin tarayya ‘Federal Medical Centre’ (FMC) dake Jabi ta maya gurbin ma’aikatan jinya na asibitin da ke yajin aiki a karkashin inuwar kungiyar JOHESU da wasu sabbin ma’aikata.

Shugaban kungiyar likitoci na babban birnin tarayya Abuja (NARD) Arikawe Adeolu ne ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba.

Adeolu yace yin hakan da asibitin ta yi ya zama dole ganin cewa rashin ma’aikatan jinya na kawo wa likitoci cikas a asibitin tun da suna ta yajin aiki.

“Ko dayake kashi 80 bisa 100 na aiyukkan da ake yi a asibitin ya ci gaba amma aiki na yi wa likitoci yawa musamman yadda wasu kan kwana suna aiki.”

Adeolu ya yi kira ga sauran asibitocin mallakin gwamnati dauki sabbin ma’aikata da za su na rika taimaka musus wajen gudanar da ayyukan su.

” Kamata ya yi a jinjina mana kan yadda muka maya gurbin ma’aikatan jinya dake asibitin mu da wasu ma’aikatan domin rage wa likitocin mu aiki.”

A karshe Adeolu ya yi kira ga kungiyoyin likitoci na NARD da NMA da su hada hannu da gidajen jaridu domin sanar wa mutane yadda yajin aikin JOHESU ke kokarin ya gurguntar da fannin kiwon lafiyar kasar nan da yi musu gargadi da su toshe kunnuwan su daga sauraren karerayin da JOHESU ke ta sheka wa don a tausaya musu.

Share.

game da Author