Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumomin kula da walwalar alhazai na jiha za su sanar da kudin tafiya aikin hajjin bana wanda hukumar NAHCON ta amince da shi.
NAHCON ta bayyana cewa ta kammala shiri taf domin sun sanar da kudaden nan ba da dadewa ba.
Wani babban ma’aikacin hukumar wanda baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa NAHCON ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki a hukumar domin ganin ba sake fadawa matsalolin da ta yi kokuwa da su a aikin hajji na bara ba.
” NAHCON za ta yi kokarin ganin ta kudin tafiya aikin hajji a bana bai bambamta da na bara ba duk da cewa kasar Saudi ta yi wasu ‘yan karin kudade.”
A jihar Kaduna kuwa tuni hukumar ta bayyana kudin aikin a bana.
Mai kula da harkokin hukumar a jihar Imam Dantsoho ne ya sanar da haka wa manema labarai a ofishin hukumar dake Kaduna ranar Laraba.
Dantsoho ya bayyana cewa Hukumar alhazai na kasa NAHCON ta amince wa maniyyata a jihar Kaduna su biya Naira miliyan (N1,490,615.05).
” Hakan ya nuna cewa maniyyatan bana sun sami ragin Naira 44,615 idan aka kwatanta kudin bana da na bara.”
Sannan kuma a bana kowace jiha ce za ta fidda kudin kujera ga maniyyatan ta.