Gwamnatin Buhari ta kore ni saboda na ki tsayawa binciken ‘yan adawa kadai -Mai Binciken Musamman

0

Wani kwararraren mai binciken harkallar kudade na musamman da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka sojan-hayar binciken kudaden da gwamnatin baya ta wawura, ya ragargaji gwamnatin bayan ta kore shi daga aiki.

Victor Uwajeh ya ce an ba shi umarni ne ya rika binciken ‘yan siyasar da ke adawa da gwamnatin Buhari kawai a cikin binciken sa da ya rika yi, na zakulo masu kadarori da gidaje a kasashen waje.

Mai binciken ya ce shi fa kwata-kwata bai amince a sa masa sharuddan binciken wasu kuma ya kauda kai daga wasu duk munin laifin su ba.

Sai dai kuma gwamnatin ta ce karya Uwajeh ke yi, an kore shi ne saboda an gano shi ma akwai guntun kashi a jikin sa.

An dauki Uwajeh sojan hayar fallasa masu kadarori ne a kasashen waje, a cikin watan Maris, kuma ya yi rawar gani wajen fallasa masu jari da kadarori da maka-makan gidaje da kudade a Turai.

Shi ne ma a cikin watan Maris ya fallasa dimbin dukiyar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ya kimshe a Turai. Uwajeh ya fallasa wa ‘yan jarida, kuma aka fallasa Ekweremadu.

Uwajeh dai mazaunin Landan ne, kuma da farko EFCC ce ta dauke shi sojan-haya, sannan kuma Kwamitin Shugaban Kasa kan Gano Dukiyar da aka Sace, a karkashin Okoi Obono-Obla ta dauke shi aiki.

Uwajeh na cikin aikin san a fallasa wadanda suka tara dukiya a Turai, sai katsam aka ce an kore shi a karshen watan Afrilu, a bisa zargin shi ma ya na da hannu a wasu harkalloli da suka jibinci yaudara.

Sai dai Uwajeh ya ce karya ake yi masa, Sanata Andy Uba ne ke yi masa bi ta da kulli, saboda ya na bin Sanatan bashin dala milyan 9, da ya ki biyan sat un wani aiki da ya yi masa cikin 2012.

Magana ta fara yin zafi tun bayan da Uwajeh ya ki bayyana a wata kotu dangane da wani beli da ya ke da hannu.

An rubuta masa wasika, kuma an buga a jaridu cewa ana neman sa kotu, amma bai je ba. A kan haka ne mai shari’a ya ce to a kamo masa shi idan an yi arba da shi.

Jiya Talata Uwajeh ya fitar da takarda daga Landan, ya ce an kore shi daga aiki ne saboda an ce ya maida hankali kan ‘yan adawa kadai, amma ya ce shi bai yarda ba.

“A lokacin taron Kasashen Duniya da Ingila ta Rena wanda aka yi a Landan cikin watan Afrilu, wasu jami’an Najeriya sun zo sun same ni a nan Landan, su ka kafa min sharuddan da ni kuma na ce ban yarda ba. Dalili kenan aka soke yarjejeniyar aikin da na ke yi wa gwamnatin Buhari.”Inji Uwajeh.

Uwajeh y ace an turo masa sunayen mutane da dama wadanda duk masu adawa da wannan gwamnatin ne, shi kuma ya ce dole sai an hada da wadanda ke cikin gwamnati, tunda ga su nan da dama an san sun wawuri kudade, amma aka ce babu ruwan sa da su.

An tuntubi Obla ammma duk ya karyata zargin da Uwajeh ya yi.

Share.

game da Author