JAMB ta tara Naira biliyan 8.5 daga siyar da fam din Jarabawar shiga jami’o’i

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Kasa (JAMB) ta bayyana cewa bana hukumar ta tara Naira biliyan 8.5 daga siyar da fom din jarabawar shiga jami’o’i.

Wani jami’in hukumar da baya so a fadi sunan sa ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES ranar Juma’a a Abuja.

” Hukumar ta tara wadannan kudade ne daga cinikin fom din da dalibai 1,602,762 suka siya sannan da wasu dalibai 135,670 da suka siya fom din na ‘Direct Entry’.”

“Kowanen su ya biya Naira 5,500 wanda Naira 4,700 ya shiga aljihun mu sannan Naira 800 ya shiga aljihan bankunan da suka karbi kudaden.”

Bayan haka jami’in ya ce duk da wannan cinikin da suka samu bana hukumar ta sami ragowar daliban da suka siya fam din.

” An samu nasarar hakane yiwu ne saboda hubbasan da Sabon Shugaban hukumar Ishaq Oloyede ya ke yi tun da ya hau kujeran shugabancin hukumar.”

Ya ce ko daya ke bai san adadin yawan kudaden da hukumar za ta saka a asusun gwamnati ba.

A Karshe shugaban hukumar Ishaq Oloyede ya yi kira ga gwamnati da ta basu damar biyan ma’aikatan su domin haka zai kawar da matsalolin wasushe kudade da ma’aikatan hukumar ke yi.

Bayan haka yace hukumar za ta bukaci Naira biliyan 4 don gyara ofisoshin ta dake jihohin kasar nan da hedikwatar ta da babban birnin tarayya Abuja.

Share.

game da Author