Mai gabatar da shaida Sambo Maina, ya bayyana wa Mai Shari’a A. R. Mohammed na Babbar Kotun Tarayya cewa yadda Andrew Yakubu ya kimshe dala miliyan 9.77 ya kimshe a gidan sa na Kaduna.
Sambo Maina, wanda jami’in EFCC ne ya bayyana wa Mai Shari’a haka a cikin wani fam na gabatar da shaida mai dauke da bayanin.
Ya kara da cewa tsohon shugaban NNPC din ya kasa yin bayanin yadda aka samu wasu kudi har fam 74,000 a gidan sa.
Da ya ke bayyana yadda har EFCC suka samu fam din na rantsuwar mallakar kadarori, Sambo ya ce “Mun fara binciken wasu kwangiloli iri biyu ne na NNPC.
“Kwangilar farko ita ce ta wata yarjejeniya tsakaninn NNPC da NPDC da wani kamfani wai shi Atlantic Energy Drilling Concept Ltd.
Ya ce sun afka bincike ne bayan samun rahoton da EFCC ta yi, na zargin karkatar da wasu kudade daga Asusun Atlantic Energy Drilling Concept na Najeriya, zuwa wani Asusun kamfanin na Switzerland. Akwai ma wasu kudaden da sake karkatarwa zuwa tsakanin wasu kamfanoni biyu.
“A kan haka ne muka gayyaci Andrew Yakubu da ya zo ofishin mu ya yi amana karin haske”. Inji Maina.
Bayanin da ya yi mana ne muka gano cewa a lokacin da ya ke shugabancin NNPC ne aka karkatar da kudaden.
Ya ce bayan Yakubu ya yi bayani, sai kuma ya cike fam na bayanin adadin dukiya da kadarorin da ya mallaka tsakanin Juni zuwa Agusta, 2015.
An daga sauraren shari’ar zuwa ranar 3 Ga Yuli, 2018.
An dai samu makudan kudaden ne a gidan Andrew Yakubu na Kaduna, wadanda shi kuma ya ce duk kyauta ce ya rika samu daga ‘yan uwa da abokan arziki.