Za a gwada maganin Ebola a Kasar Kongo – WHO

0

Jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya Peter Salama ya bayyana cewa da yiwuwar hukumar za ta gwada ingancin maganin rigakafin cutar Ebola da ake kira ‘rVSV-ZEBOV’ a kasar Kongo domin hana cutar yaduwa zuwa wasu kasashe.

Ya ce koda yake amfani da maganin na da wuya sannan maganin ba kare mutum zai yi ba gaba daya daga cutar amma suna fatan cewa gwamnatin kasar za ta basu damar gwada wannan magani a kasar.

Idan ba a manta ba ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kongo ta sanar cewa cutar ta yi ajalin mutane 17 a kasar sannan an sami tabbacin bullowar cutar ne a kauyen Ikoko Impenge’’.

Ya ce a dalilin kusancin garin Kinsasha da kauyen Ikoko Impenge wannan matakin ya zama dole a yi amfani da ita.

A karshe ma’aikatar kiwon lafiyar kasar na Kongo ta ce za ta aika da kwararrun likitoci zuwa yankin arewa maso gabashin kasar domin gano ainihin sanadiyyar bulowar cutar.

Share.

game da Author