Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane 101 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa a Najeriya.
Hukumar ta sanar da haka ne ranar Lahadi bisa ga binciken da ta gudanar inda ta kara da cewa a yanzu haka suna da tabbacin mutane 408 na dauke da cutar daga jihohi 20 a kasar nan.
Jihohin kuwa sun hada da Abia, Anambra, Bauchi, Benue, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Abuja, Gombe, Imo, Kogi, Lagos, Nasarawa, Ondo, Osun, Plateau, Rivers da Taraba.
” Bayan haka kuma mutane da dama na kan siradin iya kamuwa da wannan cuta dalilin cudanyar da suka yi da wadanda suka kamu da cutar a wadannan jihohin.”
Ya ce akalla mutane 4480 ne ka kan wannan siradi.
A karshe wani kwararren likita Oyewale Tomori ya yi kira ga gwamnati da ta canza matakan dakile yaduwar wannan cuta. Cewa yin hakan zai taimaka wajen kawar da cutar gaba daya daga kasar nan musamman yadda ta fi yaduwa da yin ajalin mutane a wannan shekarar.