KIRA GA IYAYE: Yin rigakafi ga ‘ya’yan mu shine mafita, Cewar Ministan Kiwon Lafiya

0

Karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi shirin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafin cututtuka cewa hakan na da matukar mahimmanci domin bayan ceto rayukan yaran, wato nisanta su da ga kamuwa da cuta, sannan hakan zai sa ba za a kashe kudade ba domin siyan magani.

Ehanire ya yi wannan kira ne a taron tunawa da ranar kiwon lafiya ta duniya wanda aka yi ranar 7 ga watan Afrilu a Abuja.

” Kamata ya yi mutane su gane cewa yi wa ‘ya’yan su alluran rigakafi ya fi shan magani muhimmanci domin haka zai samar wa yayan ka da kariya ne daga cututtuka tun kafin su kama su sannan zai rage mace-mace da kashe kudade wajen meman magani.”

Ya kuma ce duk da cewa samar da ingantaciyyar kiwon lafiya wa kowa a kasar nan zai dauki tsawon lokaci, gwamnati na iya kokarin ta don ganin wajen ganin ta samar wa ‘yan kasa ingantacciyar kiwon lafiya ta hanyar gyara cibiyin kiwon lafiya a kasa baki daya.

” Idan gwamnati ta gyara cibiyoyin kiwon lafiyar kasar nan su kuma za su dawama ne akan wayar da kan mutanen game da mahimmancin tsaftace muhalli,hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cututtuka, cin abincin da za su kara karfin garkuwan jiki da sauran su.”

A karshe Jami’in Kungiya kiwon lafiya ta Duniya (WHO) Wondi Alemu ya jinjina wa gwamnatin tarayya kan kokarin da take yi wajen ganin ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya a kasar.

Ya kuma yi kira ga mutanen kasa da su yi amfani da wannan dama da gwamnati za ta samar don inganta kiwon lafiyar su da na ‘ya’yan su.

Share.

game da Author