Matsalar tsaro a kasar nan abin damuwa ce kwarai–Gowon

0

Tsohon Shugaban Kasa, Yakubu Gowon, ya bayyana matukar damuwar sa dangane da yadda ake ta kara samun kalubalen tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Gowon ya yi wannan jawabi ne yayin ganawa da manema labarai a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, inda ya ce bayan Yakin Basasa, ya sha yin addu’a kada Najeriya ta sake afkawa cikin irinn wannan mawuyacin halin.

Gowonn ya ce mummunan kashe-kashen gungun ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban, Boko Haram da kuma fadan makiyaya da manoma, abin damuwa ne matuka ga shugabanni da iyayen kasa da kuma jama’a baki daya.

Ya tabbatar da cewa shugabanni na fama da gaganiyar ganin an kawo karshen wannan kashe-kashe a fadin kasar nan.

Ya kara jimamin ganin irin yadda aka wayi gari mutane ke nuna rashin tausayi a kan al’umma, ta yadda a yau an maida ran mutm ba bakin komai ba.

Ya yi kiran a kara bai wa shugabanni goyon baya domin su ma a kullum ba shantakewa suka yi su na barci ba. Ana ta kokarin ganin an kawo karshen kashe-kashen ne a koda yaushe.

Share.

game da Author