Da safiyar yau Litinin ce Sanata Dino Melaye ya bayyana a shafin sa na tiwita cewa ‘yan sandan Najeriya sun cafke shi a lokacinn da ya ke kokarin tafiya kasar Morocco domin halartar wani taro.
Ya ce an cafke shi bayan ya kammala hidindimu a cikin filin jirgin saman Nnamdin Azikwe da ke Abuja, a lokacin da ya ke kokarin ya tafi ya hau jirgi.
Tun cikin watan da ya gabata jami’an tsaro suka bada sanarwar cigiyar neman sa da ake yi dangane da binciken da ake a kan sa na wata shari’a wadda a yanzu haka ta na kotun Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Neman da ake yi masa na da nasaba da zargin hannun da ya ke da shi a wani kisan kai, da kuma ikirarin da wasu mahara suka yi cewa shi ne ke ba su makamai.
Discussion about this post