WHO ta tallafa wa kananan hukumomin Kaduna da Babura

0

Jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) Dauda Madubu ya bayyana cewa kungiyar ta tallafa wa kananan hukumomin jihar Kaduna da baburan hawa domin sauwake zirga-zirga ga ma’aikatan kiwon lafiya a kauyukan jihar.

Madubu ya kuma yi kira ga ma’aikatan da su dinga hada kai da sarakunan gargajiya a duk inda suke aiki domin samun nasara a aikin da suke yi.

A karshe babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kaduna wanda ya karbi baburan a madadin kwamishinan kiwon lafiya ya tabbatar da cewama’aikatar a jihar za ta yi kokarin ganin ta samu nasara a aikin samar wa mutane kiwon lafiya a ko-in a fadin jihar. Sannan ya ayi amfani da wannan kyauta kamar yadda WHO ta bukata.

Share.

game da Author