Kungiyar Likitocin ido za ta yi wa yara gwajin ido kyauta a Najeriya

0

Wata kungiyar likitocin ido ta Najeriya (NOA) ta bayyana cewa za ta yi wa yara ‘yan shekara 5 zuwa 14 gwajin cututtukan ido kyauta a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar Ngozi Nwanekezie ta ce za suyi haka ne domin taimakawa yara musamman wadanda ke fama da ciwo ido.

Dalilin cikar kungiyar shekara 50 da kafuwa ne ya sa za su bada wannan gudunmuwa ga yara masu tasowa wanda sune ” Manyan Gobe.”

Share.

game da Author