Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama ‘yan sara suka 70 da suka addabi mutane a jihar musamman mazauna unguwannin Kawo, Badarawa, Unguwan Dosa da sauran sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Austin Iwar ne ya sanar da haka a hedikwatan rundunar a Kaduna da yake ganawa da manema labarai ranar Juma’a.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta kawo muku labarin yadda wadannan ‘yan ta’adda da aka yi wa lakani da ‘Yan shara suka kai wa unguwanin Kwaru, Badara da Kawo hari inda sanadiyyar haka wani tsohon soja a unguwan Kwaru ya rasa hannun sa sannan suka kona gidajen mutane.
Kwamishina Iwar ya ce yaran da suka kama basu wuce ‘yan shekaru 18 zuwa 25 da haihuwa ba.
” Mun kama su da makamai da ya hada da gariyo, Takubba, adduna, kokara, fatefate, tsitaka, babura uku, kayan sojoji, kwari da baka da dai sauran su, sannan yanzu haka suna tsare ana gudanar da bincike kafin a gurfanar dasu gaban alkali.
A karshe kuma ya yi kira ga mutane da suke ajiye da makaman da ba su da lasisi da su gaggauta mika su ga jami’an tsaro kafin lokacin da aka bada domin haka ya cika.