Fitaccen dan siyasar nan dan asalin jihar Kaduna Datti Baba Ahmed ya bayyana ra’ayin sa na yin takarar shugabancin kasar nan a 2019.
Datti wanda dan asalin jihar Kaduna, ya tsunduma cikin harkar siyasa ne tun a shekarar 2003 in da ya wakilci karamar Hukumar Zaria a majalisar wakilai a jam’iyyar ANPP. Daga nan kuma sai ya sake koma wa majalisar tarayya din amma wannan karon bayan ya kada tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi a takarar sanata.
Datti ya kafa jami’ar baze dake Abuja sannan yana da wasu kamfanoni da ya dibi matasan Najeriya sama da 600 suna aiki a wadannan kamfanoni.
Datti yayi karatu a manyan jami’o’in da ake ji da su a duniya da ya hada da jami’ar Westminister, dake kasar Britaniya da manyan makarantu kamar su London Business school da Harvard.
Datti ya ce lokaci yayi da matasa masu jini a jika za su dare kujerun shugabanci a kasar nan.
Discussion about this post