An kashe ‘yan gudun hijira bakwai a jihar Nasarawa

0

Shugaban kungiyar matasan kabilar Tiv reshen jihar Nasarawa Peter Ahemba ya koka kan kisan gillar da wasu mahara da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wasu ‘yan gudun hijira bakwai a kauyen Ihukan dake karamar hukumar Awe a jihar.

Ahemba ya bayyana haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Lafiya.

” Maharan sun shigo kauyen Ihukan ne da niyar satan kayan abinci amma da suka hadu da wadannan ‘yan gudun hijira sai suka kashe su.

” Ina kuma kira ga kabilan tiv dake wannan jihar da su kwantar da hankalinsu ganin cewa mun kai karan wannan mummunar aiki ga jami’an tsaro.” Inji Ahemba.

Share.

game da Author