Kwamishinar harkokin kasuwanci na jihar Kaduna Ruth Alkhali ta bayyana cewa gwamnati ta horas da matasa 540 sana’o’in hannu dabam-dabam a shirin ta na samar wa matasa aikin yi a jihar.
Alkhali ta fadi haka ne ranar Laraba a taron yaye matasan da suka kammala horon a Kaduna.
” Matasan da muka horas sun hada da nakasassu wadanda basu taba shiga makarantar boko ba, wadanda suka kasa kammala makarantar boko da almajirai sannan mun zabo su ne daga kananan hukumomin Kaura, Sabongari da Igabi.”
” Sana’o’in suka koya sun hada da dinki, walda, kafinta, dabarun jinya, kera karafuna da sauran su.”
Bayan haka gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa matasan jihar don inganta rayuwar su.
A karshe kakakin majalisar dokokin jihar Aminu Shagali ya ce majalisar jihar zata ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya wajen ganin matasan jihar sun sami horo nagari.