Muna tattaunawa da JOHESU don biya musu bukatun su – Ministan Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba kungiyar ma’aikatan jinya ‘JOHESU’ za ta dakatar da yakin aikin da ta fara kwanaki 5 da suka wuce.

Ya fadi haka ne ranar Laraba da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya bayan kammala taron kwamitin zartarwa a Abuja.

Adewole yace gwamnati ta kafa kwamiti da a yanzu haka yana tattauna hanyoyin da suka fi dacewa a bi domin biyan bukatun kungiyar JOHESU.

” Tabas JOHESU ta bayyana mana bukatun ta a wata zama da muka yi amma har zuwa yau ba a kai ga matsayin biyan bukatun ba tukuna.”

” Sannan duk da wannan korafe korafen da suke yi, cikin bukatu 15 da suka lissafo mana gwamanti ta iya biyan 14 a cikin shekara daya da rabi kuma muna iya kokarin mu wurin ganin mun biya cikon na 15 din.”

Bayanai sun nuna cewa yajin aikin JOHESU wanda ke neman ya gurgunta fannin kiwon lafiyar kasar nan na cikin kwanaki na tara kenan.

Share.

game da Author