Yadda Majalisar kasa da hadin bakin Minista Kemi suka wawuri naira biliyan 6.6 don siyan sabbin motoci

0

Majalisar tarayya dai ta dade tana kutsa kan ta cikin kamayaya da harkallar biliyoyin kudade da ba a san inda ake yi dasu.

A rahoto na musamman da PREMIUM TIMES ta buga, ta bankado wasu harkallar naira biliyan 10 da aka kakkasa su kamar watandar naman karamar sallar, inda kowa ya kwashi kason sa ya kara gaba.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa kamfanoni 44 da Saraki da Dogara suka gabatar wa Kemi Adeosun wato Ministan kudi daga cikin 82 din nan, ba su ma da rajista da Hukumar Kula da Kwangiloli ta Kasa, kuma babu su a cikin jerin Kididdigar ‘Yan Kwangila ta Kasa da suna suka yi wadannan kwangiloli.

Karin bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa wasu 17 ma daga cikin 44 din ko rajista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ba su da ita.

Dukkan bangarorin Saraki da Dogara da PREMIUM TIMES ta tuntuba, sun kasa cewa komai.

Binciken da wakilinmu a Majalisa ya gudanar, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan kwangilar a gaskiya sun yi ayyukan, amma fa tuni an rigaya an biya su tun tuni, amma kuma an jefa sunayen su a cikin wadanda aka ce wai su na bin bashi.

Yanzu kuma wata sabuwa ce aka sake buduwa domin kuwa majalisar da hadin bakin ministar kudi, Kemi Adeosun suka sake fidda wasu makudan kudi har naira biliyan 6.6 domin siyan motoci wa ‘yan majalisar.

Kamfanonin da aka ba wadannan kwangiloli ko lasisi wasu basu da shi sannan abin tambaya anan, shin suna bukatar irin wadannan kudade a irin halin da kasa ta fada na karayar tattalin arziki?

Wannan kudi ya fi kudin da aka ware wa fanni tsaron kasa a kasafin kudi na 2018, sannan kuma za a iya wadata kauyuka 660 da ruwan sha idan aka gina rijiyoyin burtsatse kan kowani daya naira miliya 10.

Wannan kudi ya fi kudin da aka ware wa ma’aikatar harkokin mata, da wanda aka ware wa hukumar NACA da dai sauran su.

Karanta nan: EXCLUSIVE: How Saraki’s National Assembly spent N6.6billion Adeosun largesse on exotic cars

Ga sunayen kamfanonin da suka yi kwangilar siyan motocin.

Share.

game da Author