Ministar kudi, Kemi Adeosun da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun maida martani ga PREMIUM TIMES dangane da labarin da aka buga jiya safiyar Juma’a, mai take: “Yadda Minista Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar suka yi wa naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya.”
Da ta ke maida martani, Kemi Adeosun ta bayyana labarin da aka buga da cewa “karya ce, kuma ba a yi bincike ba.”
Kakakin yada labaran ministar, Oluyinka Akintunda, ya bayyana cewa sun yi mamakin ganin yadda PREMIUM TIMES ta buga labarin a matsayin minista ta bayar da kudaden ba bisa kan ka’ida ba.
A cikin wata takarda da ya sa wa hannu a madadin ministar, Akintunda ya ce kudaden da ministar ta bayar duk kan ka’ida aka bayar da kudaden, kuma har ma sai da Kwamitin Duba Cancantar Biyan Kudade ya zauna ya duba, kafin a biya kudin.
“Ministar da kan ta ce ma shugabar kwamitin, don haka kuma kafin ta bada umarnin a cire kudaden, sai da aka aiko mata da takardar neman a fitar da kudin, ba haka kawai da ka ta fitar da su ba.”
Ministar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da abin da PREMIUM TIMES ta buga, ta na mai cewa “labarin bogi ne.”
Sai dai kuma ministar ba ta ce komai ba dangane da yadda ba a gabatar mata da bayanan da ke nuna an yi kwangilolin ba, sai kawai ta ce a fitar da kudin, kuma ba ta ce komai ba dangane za ikirarin PREMIUM TIMES, cewa kamfanoni 44 daga cikin 82 da aka bada sunayen su a matsayin wadanda suka yi kwangilar, duk na cuwa-cuwa ne.
Har ila yau, minista Kemi Adeosun ta yi shiru daga bayanin da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi cewa yawancin kwangilolin duk an yi su, amma kuma an rigaya an biya kudaden tuni, sannan daga baya kuma aka kara rattaba sunayen su aka kara biyan kudin da sunan su.
SAI NA MAKA KU KOTU -Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya yi barazanar maka PREMIUM TIMES kotu dangane da labarin da aka buga, inda aka fallasa yadda suka yi wa naira bilyan 10 rabon-tuwon-gayya.
Shi ma ya maida martani a jiya Juma’a da yamma bayan an buga labarin.
Kakakin yada labaran sa, Yusuph Olaniyoni, ya fitar da sanarwa inda Bukola Saraki ke ta jaddada cewa bai karbi wasu kudade naira bilyan goma ta haramtacciyar hanya ba.
Ya ce duk kudaden da aka karba, an karbe su ne ta sahihiyar hanya. Kuma bangaren da wannan alhaki ya rataya a wuyan sa, shi ke karbar kudin ba Saraki ko Dogara ba.
Ya ce labarin da aka buga karya ce kuma an nuna rashin iya bincike a cikin labarin.
Sai dai ya tabbatar da cewa ya na da masaniyar za a buga labarin, domin an tuntube su domin a ji ta bakin sa, tun kimanin makonni uku da suka gabata.
Ya ce an hada PREMIUM TIMES da bangaren majalisa masu kula da gudanar da ayyuka a majalisar, inda bangaren ya ce a saurare su, za su bada amsa.
“Mun yi mamakin yadda PREMIUM TIMES ta yi gaggawar buga labarin, ba tare da jiran amsar da za a ba ta ba.”
Shi ma Saraki ya yi kira da kada wanda ya dauki labarin a matsayin gaskiya, karya ce kawai da kitsa sharri, kuma ya ce zai garzaya kotu tunda abin ya kai ga bata masa suna.
Sai dai shi ma kamar Minista Kemi, bai ce komai ba dangane da batun barankyankyamar kamfanonin bogi da kuma yadda aka biya kudaden da sunayen wasu kamfanonin da an rigaya an biya su kudaden aikin da suka yi tun can baya.