El-Rufai ya bace, bashi babu labari sa – PDP

0

” Kusan makonni biyu Kenan rabon da a ga wulkawar gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai a Jihar dama kasa baki daya.

” Abin ya tada mana hankali matuka ganin cewa babu wanda yake cewa komai game da hakan.” Inji PDP

Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Hassan Hyet ne ya yi Kira ga jama’a da su taya su nemo gwamna El-Rufai.

PDP ta ce maimakon El-Rufai ya yi yadda doka ta gindaya na mika takarda wa majalisar Jihar domin amince wa mataimakin sa Barnabas Bantex ci gaba da gudanar da ayyukan mulki a jihar amma bai yi haka ba.

Jam’iyyar PDP ta kara da cewa hakan da yayi dumulmula tsarin siyasa ne da karya dokar Kasa. ” Ya yi tafiyar sa, shi bai mika wa mataimakin sa ragamar mulki ba, shi bai ce wa kowa komai ba ana ta watangaririya a Jihar kusan makonni biyu kenan.

Share.

game da Author