Gwamnan Jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya ba jami’an tsaro a Jihar oda da su harbe koma waye a ka gani dauke da makami, ba ma sai har an kama shi ba.
Yari ya furta haka ne a ziyarar jaje da ya kai wa mutanen karamar hukumar Anka, a fadar sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmed.
Idan ba a manta ba wasu mahara sun far wa kauyen Bawan Daji dake karamar hukumar Anka inda suka yi fashi sannan suka kashe mutane har 30.
Gwamnan Yari ya ce wannan umarni ne daga shugaban Kasa da kan sa da shi gwamnan.
Bayan haka kuma ya tsige wasu dakatan wasu kauyuka biyar dake yankin cewa ana zargin su da ba ‘yan ta’adda mafaka a wuraren su.
Ya Kara da cewa wannan hare-hare da kashe-kashe ya wuce misali dole ne a fatattaki wadannan bata gari.
Da yake nasa bayanin, Sarkin Anka ya roki gwamnan da a Karo wa Jihar da yankunan Jihar Jami’an tsaro.
” Akwai karancin Jami’an tsaro da muke fama dashi a Jihar nan, muna rokon Mai girma gwamna da a karo jami’an tsaro zuwa yankunan mu.”