An kama wasu barayin shanu a daidai suna raba danyen nama a dajin Mambilla

0

Dakarun Soji da ke sintiri a dazukan tsibirin Mambilla, na karamar hukumar Sardauna, Jihar Taraba, sun kama wasu barayin shanu a daidai suna raba danyen naman shanu da suka yanka a cikin daji.

Bayan haka sun nuna Inda suka boye wasu shanu har 30 da suka sace a wata maboya da suke da ita a dajin.

Wadanda aka kama sun hada Hammanjulde Yahya, 50, Umaru Yahya, 40, Paul Samuel, 35, Juli Adamu, 30, Ibrahim Yusufa, 27, and Usumanu Buba, 25.

Jami’an tsaro sun yi kira ga duk wanda ya San cewa akwai shanun da ba nasa na a tare da shi ya gaggauta dawo da su in ba haka ba zai ko dandana kudar sa.

Share.

game da Author