Ko majalisa ta so ko ta ki, za mu ci gaba da neman bashin nan har sai mun samu

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa duk da kin saka mata hannu da majalisar Dattawa ta yi ta samu bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya,ba zai hana ta ci gaba da ayyukan raya Jihar da take yi ba sannan za ta kara tamke kugunta bar sai ta cimma burin ta.

Kwamishinan Kudi na Jihar Suleiman Abdu Kwari, ne ya furta haka da yake zantawa da manema labarai a garin Kaduna.

Kwari ya ce hujjojin da sanatocin Jihar uku suka bada ba gaskiya ba ne sannan hakan da suka yi ba zai hana Jihar daga ci gaba da neman wannan bashi ba.

” Mun cika dukkan sharuddan da ake bukata a cika tun daga na bankin duniya bar zuwa wanda ake bukata majalisar ta amince, amma saboda siyasa da son kai na sanatocin Jihar uku sun ki mara wa kokarin Jihar baya ta samu wannan bashi.

” Hasali ma idan ba a manta ba majalisar wakilai sun amince da wannan kudiri tun kwanakin baya, duk saboda sun ga lallai mun cika sharuddan da ake nema.

” Wannan bashi za muyi amfani da shi ne wajen inganta rayuwar mutane Jihar Kaduna, musamman a fannin Ilimi, Kiwon Lafiya da sauransu. Mutanen Jihar Kaduna shaida ne cewa wannan gwamnati ba gwamnatin kasa mu raba bane, gwamnatin talakawa ne kuma gwamnatin aiki.

A karshe Kwari ya ce Kaduna yanzu ba irin da ba ne, gwamnatin yanzu gwamnatin aiki ne ba na watanda ba, saboda haka suna nan kan bakan su.

Share.

game da Author