Shugaban kwamitin zartarwa na kamfanin Biovaccines, Oyewale Tomori ya ce nan da shekaru uku zuwa hudu kasuwanin Najeriya za su cika da alluran rigakafin da aka sarrafa a kasar nan.
Za a fara samun magungunan ‘yar kasa ne nan da shekara hudu masu zuwa.
Kamfanin Biovaccines wani bangaren kamfanin ‘May&Baker Nigeria Plc’ ne ta hada guiwa da gwamnatin tarayya don bude kamfanin yin alluran rigakafi a kasan.
Tomori ya bayyana cewa za su yi aiki da kwararrun likitoci ne don ganin sun sami nasarar wannan abu da suka sa a gaba.