Ranar Talata a Abuja ne kasar Amurka ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta maida hankali wajen ganin ta samar da tallafi na kudin magani domin taimakawa masu fama da cutar kanjamau a kasar.
Kasar Amurka ta ce hakan ya zama dole idan har Najeriya na so ta kawar da cutar nan da shekarar 2030.
” Mafi yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya na samun magani ne daga tallafin da kungiyoyin bada tallafi na kasashen duniya sannan siyan magungunan da wasu bukatun kiwon lafiya duk mutanen kasan ke biya.”
Bayan haka jami’ar PEPFAR Shirley Dady ta ce biyan kudaden magungunan mutanen dake dauke da cutar kanjamau da gwamnatin Najeriya za ta yi zai taimaka wajen buda wa wasu mutanen hanyar samun tallafin da suke bukata.
Daga karshe jami’in UNIADS Erasmus Morah yace yayin da Najeriya ke kokarin yin haka kamata ya yi ta tsara hanyoyin da za su tabbatar cewa wadannan kudi da za su ware an yi amfani da su ta hanyoyin da ya kamata.