Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa daliban makarantar #Dapchi 76 ne kawai Boko Haram ta saki ba duka 110 da suka dauke ba.
Ganau a garin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yau Laraba da sanyin safiya aka ga Boko Haram sun shigo garin Dapchi sun sauke daliban.
Lai ya kara da cewa ba a mika #yan matan ga kowa ba, Boko Haram sun ajiyesu ne kawai suka kama gaban su sannan za a sanar da halin da suke ciki da zaran an san yawan wadnda da aka saki.